Hukumar FA ta nemi a dage zaben FIFA

 David Bernstein Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban Hukumar FA ta Ingila David Bernstein

Hukumar kula da kwallon kafa ta Ingila FA, ta yi kira ga FIFA da ta dakatar da zaben shugabancin da ake shirin gudanarwa gobe.

Hukumar ta FA ta dauki matakin ne saboda zargin cin hanci da rashawar da ya dabai-baye Hukumar ta FIFA.

Shugaba mai ci Seff Blatter ne kawai yake takara a zaben bayan da Muhammad Bin Hammam ya janye daga takarar.

Shugaban FA David Bernstein, ya ce wannan kiran ya zama wajibi bayan da a ranar 19 ga watan Mayu, Hukumar ta ce ba za shiga cikin zaben da za a yi ba.

"Abubuwan da suka faru a 'yan kwanakin nan, sun karfafa tunanin da muke da shi, don haka muna kira ga sauran hukumomin kwallon kafa na kasashe su goyi bayanmu domin aiwatar da abu biyu.

"Na farko, a dakatar da zaben domin a baiwa tsarin cikakkiyar martaba, ta yadda wani dantakarar da zai iya kawo sauyi zai samu damar tsayawa takara.

"Na biyu, a kafa wata hukuma daga waje da za ta bada shawara kan yadda za a gyara hanyoyin tafiyar da al'amura a FIFA, inda kowa da kowa zai samu damar fadar albarkacin bakinsa.

Masu bada tallafi sun koka

Manyan masu tallafawa hukumar dake kula da kwallon kafa ta duniya FIFA wato kamfanonin Coca Cola dana Adidas sun nuna damuwarsu akan irin takaddamar da ta kewaye hukumar kwallon kafar.

Kamfanin Cola Cola ya ce zargin cin hanci abu ne mai takaici, yayin da shi ma kamfanin Adidas ya ce wannan ba abu ne mai kyau ga harkar kwallon kafa ba, balle ga hukumar kanta.

Shi ma kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Emirates, wanda ke daukar nauyin gasar cin kofin duniya, ya ce baiji dadin abinda ke faruwa a Hukumar ta FIFA ba, yana mai kira da a gudanar da bincike.

Shugaban hukumar Sepp Blattter ya musanta batun cewa hukumar na cikin rikici, inda ya ce koma da hakan ne, hukumar zata iya warware matsalardta da kanta.

Sai dai fitar da jawaban da kamfanonin Coca Cola da na Adidas suka yi na tabbatar da cewa hukumar kula da kwallon kafar na da matsala, wadda kuma za su so ganin an warware ta.

Karin bayani