Juventus ta nada Conte a matsayin Koci

conte Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Antonio Conte

Juventus ta kulla yarjejeniya da tsohon kyaftin dinta Antonio Conte don maye gurbin Luigi Delneri a matsayin koci.

Dan shekaru arba'in da daya din ya sanya hannu a kwangilar jan ragamar kungiyar zuwa shekara ta 2013.

Conte dai shine ya jagoranci Siena ta kara komawa gasar Serie A kamar yadda yayi a Bari a shekara ta 2009.

Sai dai golan Juventus Gianluigi Buffon yayi gargadin cewar kada mutane sa sanya dogon buri a Conte.

Conte ya bugawa Juve wasa a karawa 296 inda ya lashe kofina serie A biyar da kuma gasar zakarun Turai a shekarar 1996.

Tun bayan tafiyar Fabio Capello a shekara ta 2006, babu wani koci daya wuce shekaru a Juventus.