Owen na son cigaba da taka leda a United

united
Image caption Micheal Owen

Micheal Owen wanda kwangilar sa ta kare a Manchester United ya nuna sha'awarsa na cigaba da taka leda a Old Trafford.

Dan shekaru 31 din ya taimakawa kulob lashe gasar premier a karo na 19 amma bai buga wasan karshe na gasar zakarun Turai da United ta sha kashi a wajen Barcelona daci uku da daya.

Owen yace "muna da zaratan 'yan kwallo da masu lura da 'yan kwallo da gawurtaccen koci harma da magoya baya,ina saran zai cigaba".

Tsohon dan kwallon Liverpool da Real Madrid da Newcastle ya koma United ne a shekara ta 2009.

Ganin cewar akwai irinsu Wayne Rooney da Dimitar Berbatov da kuma Javier Hernandez a gaban United, da kamar wuya Owen ya samu damar taka leda a kulob din.

Ya buga wasanni 48 a Manchester United inda ya zira kwallaye 14.