Gerard Houllier ya bar Aston Villa

Gerard Houllier
Image caption Gerard Houllier ya shafe makonni yana jinya

Aston Villa ta tabbatar da cewa kocin 'yan wasanta Gerard Houllier, ya bar kungiyar bayan shafe watanni tara yana rike da mukamin.

Kocin mai shekaru 63 dan kasar Faransa bai halarci watan karshe na kakar wasan da aka kammala ba, saboda matsalar ciwon zuciyar da yake fama da shi.

An yi hasashen zai bar mukamin nasa bayan wani gwaji da aka yi masa a wannan makon.

Likitoci sun ce yana bukatar karin lokaci kafin ya murmure kuma jami'an Villa sun nuna damuwa kan cewa komawa fagen daga ka iya tayar masa da cutar.

A wata sanarwa da ya fitar, Mr Houllier, wanda ya bar aikinsa na Daraktan kwallon kafa a Hukumar Kwallon kafa ta Faransa (FFF) domin zuwa Villa, bai kawar da yiwuwar sake dawowa fagen daga ba. Ya ce: "Na yi takaici matuka cewa ba zan samu damar jagorantar Villa a kakar wasanni mai zuwa ba.