West Ham ta nada Allardyce a matsayin koci

Sam Allardyce Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sam Allardyce ya dade yana jan ragamar kungiyoyi a gasar Premier

An nada Sam Allardyce a matsayin sabon kocin kungiyar West Ham bayanda suka fada rukunin Championship daga gasar Premier ta Ingila.

Rahotanni sun nuna cewa tsohon kocin na Blackburn da Newcastle da kuma Bolton, zai sanya hannu kan kwantiragin shekara biyu domin maye gurbin Avram Grant.

Jaridar Sun ta Burtaniya ta rawaito Allardyce yana cewa: "Ina son maido da West Ham zuwa gasar Premier ba tare da bata lokaci ba.

"Zan fara aiki da zarar na kammala hutun da nake yi da iyali na."

Kungiyar West Ham ta kori Avram Grant dan kasar Isra'ila bayan da ta fada gasar Championship daga Premier.

Shi ma dai kocin riko Kevin Keen, wanda ya karasa da kungiyar zuwa wasan karshe, ya nuna aniyarsa ta jan ragamar kungiyar.