Kocin Argentina ya bata mana suna a Najeriya

grondona
Image caption Julio Grondona

Shugaban hukumar kwallon Argentina Julio Grondona ya zargi kocin 'yan kwallon kasar Sergio Batista da bata sunan kasar bayan sun sha kashi a wajen Najeriya daci hudu da daya.

Rashin nasarar Argentina din yazo ne kusan wata guda daya rage a fara gasar Copa America wanda Argentina zata dauki bakunci.

Grondona yace "ba dai dai bane a dakushe martabar babbar tawagar 'yan kwallon kasar".

Ya kara da cewar bai kamata Argentina ta saka 'yan kwallon da suka buga wasan ba tayin la'akari da cewar Najeriya ta saka zaratan 'yan kwallon ta.

Sai dai kocin Argentina Batista ya bayyana cewar ba shida matsala akan sakamakon wasan saboda ya bashi damar gano sabbin 'yan wasa.