Dan Afrika ta Kudu Pienaar ya ji ciwo

Steven Pienaar Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Steven Pienaar

Kokarin Steven Pienaar na buga wasan Afrika ta kudu tsakaninta da Masar na neman gurbin zuwa gasar cin kofin kasashen Afrika a 2012 ya gamu da cikas bayan ya turgude lokacin horo a ranar Alhamis.

Dan kwallon mai shekaru 29 yana cikin horo ne karshe ne kafin su tafi birnin Alkahira, amma sai ya fadi kasa yana rike gwiwa.

Kocin Bafana Bafana Pitso Mosimane ya bayyana cewar akwai tababa akan yiwuwar dan kwallon ta buga wasan na karshen mako.

Mosimane yace" ya samu rauni a gwiwarshi ta dama kuma yana cikin damuwa".

Yanzu dai Bafana Bafana na cikin damuwa ganin cewar manyan 'yan wasan na fama da rauni tunda Bongani Khumalo shima ba zai buga wasan ba.

Bafana Bafana ce ke jan ragamar rukunin G da maki bakwai a yayinda ya rage wasanni uku a kammala wasanni share fagen,sai kuma Masar ta karshe da maki guda.