An gano beraye a jirgin Qantas

An gano beraye a jirgin Qantas Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kamfanin Qantas yana daga cikin manya a duniya

Kamfanin jiragen sama na Qantas mallakin kasar Australia, ya dakatar da daya daga cikin jiragensa bayan da aka ga beraye a ciki.

Ma'aikatan jirgin sun ga berayen ne a wata jaka a cikin jirgin, jim kadan kafin fasinjoji su fara shiga jirgin a birnin Sydney.

Kamfanin Qantas ya bayyana lamarin da cewa na bazata ne, saboda bai saba faruwa ba.

Ya ce an bincika jirgin kuma ba a ga wata banna da berayen suka yi ba.