Kamaru ta buga canjaras da Senegal

kamaru
Image caption Indomitable Lions na Kamaru

Jami'an tsaro a Kamaru sun fesa ruwa don tawarwatsa masu zanga zanga sakamakon tashi canjaras da Indomitable Lions tayi da Senegal a wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin kasashen Afrika.

Kyaftin din Kamaru Samuel Eto'o ya barar da fenariti a minti na 87 abinda ya janyo tashin tashina a filin wasa na Ahmadou Ahidjo har sai da Etoo ya nemi afuwa.

Wadanda suka shaida lamarin sunce mutane da dama sunji rauni a lamarin daya auku a daren Asabar, inda 'yan kallo suka farfasa gilasan motoci suka yaga rigunan dake dauke da hoton Eto'o.

A hirarsa da gidan talabijin na kasar, Eto'o ya nemi ayi mashi gafara, inda kuma ya dauki laifin abinda ya faru.

Sakamakon wasan ya nuna cewar akwai yiwuwar Kamaru wacce ta lashe gasar kofin Afrika sau hudu ba zata shiga gasar da za ayi a badi ba a kasashen Equatorial Guinea da Gabon bayan ta halarci gasar sau takwas a jere.

Yanzu dai Kamaru nada maki biyar cikin karawa hudu, inda take bin Senegal wacce keda maki tara.