Fifa na binciken akan wasan Najeriya da Argentina

nigeria
Image caption Wasan da Argentina ta doke Najeriya a Afrika ta Kudu

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA tace, tana binciken zargin coge a wasan sada zumunta da aka buga tsakanin tim din kwallon kafa na kasar Argentina da kuma na Najeriya, inda Najeriyar taci Argentina hudu-da-daya.

Hukumar ta FIFA dai tace da walakin a nasarar da Najeriyar ta samu akan kasar Argentina, inda take zargin cewa, shiryawa aka yi Najeriya taci Argentina yawan wadannan kwallaye har hudu.

Mintuna biyar aka kara bayan cikar minti 90 na wasan, amma sai a karin minti takwas sannan Argentina ta samu kwallonta na farko inda Mauro Boselli.

Fifa ta ce" wannan wasan munada tababa akai".

Sai dai tuni hukumar kwallon kafar Najeriya NFF tayi watsi da wannan zargi, kuma tace zata baiwa hukumar FIFA hadin kai a binciken wannan batu ba.

Ike Uche ne ya bude fagen da zira kwallon farko minti goma da farawa sai Victor Obinna yaci na biyu ta fenariti a yayinda Uche yaci na uku kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Minti takwas da dawowa hutun rabin lokaci sai Emmanuel Emenike yaci kwallo na hudu a wasan da dan Nijer Ibrahim Chaibou yayi alkalin wasa.