Najeriya ta tashi canjaras da Ethiopia

uche Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ikechukwu Uche ne ya ciwa Najeriya kwallon farko

Najeriya ta bata rawarta da tsalle bayan ta tashi biyu da biyu tsakaninta da Ethiopia a wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin kasashen Afrika da aka buga a ranar Lahadi.

Da dama sun saran cewar Super Eagles ne zasu samu galaba a wasan da aka buga a Addis Ababa amma sai aka samu akasin haka.

Amma sai 'yan Ethiopia suka jikawa Najeriya gari karkashi jagorancin sabon kocinsu dan kasar Belgium Tom Saintfiet.

Ikechukwu Uche ne ya ciwa Najeriya kwallon farko a minti na 26 minutes kafin Saladin Seid ya farke kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Bayan an dawo kuma sai Seid ya kara cin kwallon guda a yayinda Joseph Yobo ya ramowa Najeriya.