Ina son ci gaba da takawa Ingila leda - Crouch

Ina son ci gaba da takawa Ingila leda - Crouch
Image caption Dan wasan ya zira kwallaye 22 a wasa 42 da ya bugawa kasarsa

Dan wasan Tottenham Peter Crouch ya ce ya yi tunanin daina takawa Ingila leda amma yanzu yana so ya ci gaba.

Dan wasan ya zira kwallaye 22 a wasa 42 da ya bugawa kasarsa, amma kociya Fabio Capello ba ya yi da shi.

Crouch, mai shekaru 30, ko a benci bai fito ba a wasan da Ingila ta buga 2-2 da Switzerland a wasan share fagen shiga gasar cin kofin kasashen Turai na 2012.

Amma duk da haka ya ce: "Ina bukatar ci gaba da takawa Ingila leda. Kuma ba zan fitar da rai kan bugawa kasata ba a wannan matakin. Abin alfahari ne."

Rabon da a fara wasa da shi dai tun watan Mayun 2010, sai wasan da Ingila ta kara da Montenegro a Wembley a watan Oktoba.

An dai ta shi babu ci a wasan, kuma tun daga nan aka koma a jiye shi a benci.