Koriya ta kudu ta doke Ghana 2-1

Asamoah Gyan
Image caption Asamoah Gyan ne ya zirawa Ghana kwallo dayan da ta ci

Koriya ta Kudu ta doke Black Stars na Ghana da ci 2-1 a wasan sada zumuntar da aka buga a filin wasa na Jeonju da ke Koriya.

Koriya ce ta fara zira kwallo a minti na 12 ta hannun Ji Dong-won.

Asamoah Gyan ya zubar da dama a wasan, kafin daga bisani ya ramawa Ghana a minti na 65.

Amma ana mintina kadan kafin wasan ya kare, sai Koo Ja-cheol, wanda ya shigo bayan hutun rabin lokaci, ya zira wa Koriya kwallo ta biyu.

Wannan nasara za ta kara wa Koriya kwarin gwiwa a kokarin da suke yi na farfado da kimarsu a fagen tamola.