'Hiddink zai bar Turkey'

Image caption Guss Hiddink

Hukumar kula da kwallon kafa ta Turkey ta amince cewa Guss Hiddink zai ajiye aikin shi na horon tawagar kasar, kuma akwai yiwuwar ya koma horon kungiyar Chelsea.

Wata majiya a hukumar ya ce kocin dai ba zai iya cewa Chelsea a'a ba, saboda haka mun san tabbas zai tafi.

Hiddink, mai shekarun haihuwa 64, ya jogoranci Chelsea na wucin gadi, inda ta lashe gasar cin kofin FA a shekarar 2009.

Duk da cewa dai Turkey bata taka rawar gani a wasannin share fage da ta buga na taka leda a gasar cin kofin Turai wato Euro 2012, har yanzu dai kasar bata fidda rai bayan ta buga da da daya da Belgium a ranar asabar.