Max Mosley ya soki Formula 1 kan Bahrain

Bahrain Hakkin mallakar hoto Reuters (audio)
Image caption Filin wasa na Bahrain Grand Prix a Bahrain

Tsohon shugaban Hukumar motorsport Max Mosley, ya ce ba ya tunanin za a gudanar da gasar Bahrain Grand Prix da aka shirya yi a ranar 30 ga watan Oktoba.

Gasar wacce aka shirya gudanarwa ranar 13 ga watan Maris amma aka dage a watan Fabreru saboda zanga-zangar neman tsarin dimokuradiyya, an dawo da ita ranar Juma'a.

Sai dai Mosley na ganin kimar Formula 1 za ta zube idan aka gudanar da gasar a Bahrain.

Ya shaida wa BBC Radio 5 live cewa: "Ba zan ji dadi ba idan aka gudanar da gasar. Ba na zaton kuma hakan zai faru."

Hukumar kula da gasar ta Formula 1, ta amince da gagarumin rinjaye kan dawo da gasar - wacce za a fara bude kakar wasannin da ita - kalandar 2011.

An maida gasar Indian Grand Prix, wacce ake farawa da ita a ranar 30 ga watan Oktoba, zuwa 11 ga watan Disamba.

Amma Mosley ya kara da cewa: "Wani abu da kusan kowa ke mantawa shi ne wajibi ne kungiyoyi su amince da sauyin lokutan wasan tukunna.

"Ba zai yiwu haka kawai a matsar da gasar Indian Grand Prix ba, sai an tuntubi dukkan kungiyoyin da ke cikin gasar. Akwai bukatar a samu amincewar kowa a rubuce, kuma ina ganin hakan zai yi wuya."