Shehata ya yi murabus daga Masar

Image caption Hassan Shehata

Kocin 'yan wasan kwallon kafa na Masar, Hassan Shehata ya ajiye mukaminsa na mai horar da 'yan wasan kasar.

Kungiyar kula da kwallon kafa ta kasar ta Masar ta amince da ajiye mukamin da shehata mai shekaru sittin da daya ya yi.

Duk da koma bayan da kungiyar kwallon kafar ta fuskanta a baya-bayan nan, Shehata ya bar kungiyar ne a matsayin mai horas da 'yan wasan da ya fi samun nasara a tarihin kungiyar ganin cewa ya ciyo musu kofin nahiyar Afrika har sau uku a jere.

Sai dai rashin nasarar da kungiyar ta yi a karawar da suka yi da kasar Afrika ta Kudu ranar Lahadin da ta gabata, na nuni da cewa zai yi wuya kasar ta iya kare kambunta a gasar cin kofin Afrikan da za a yi a shekarar 2012.

Kasashen biyu dai sun buga kunnen doki ne, kuma a yanzu su ne a kasan runin G, kuma ba su samu nasara ba a wasanni hudun da suka yi a rukunin.