Olympics: Tanzania ta doke Najeriya

Image caption Austin Eguaveon, kocin 'yan wasan Najeriya, 'yan kasa da shekaru 23

Tanzania ta ci gaba da taka rawar gani, a wasannin share fage na taka leda a wasannin Olympic da za'a shirya a shekarar 2012 bayan ta doke Najeriya da ci daya da nema.

Thomas Ulimwengu ne ya zura kwallon ana sauran minti takwas kafin a tashi a wasan da aka buga a Dar es Salaam.

Najeriya dai ta zura kwallaye 16 a wasanni hudu da ta buga a wasannin sharen fagen. A wasan dai da ta buga da Tanzania ta barar da kwallaye da dama.

Kocin Najeriya Austin Eguavoen ya ce yana da kwarin gwiwa Najeriya zata yi kaca-kaca da Tanzani idan sun zo Abuja, a karshen wannan wata.

Shima dai kocin Tanzania Jamhuri Kihwelu ya ce yana da kwarin kasar zata tsallake domin taka leda a wasannin Olympic din.