Arsenal ta sayi Carl Jenkinson

Image caption Sabon dan wasan Arsenal Carl Jenkinson

Arsenal ta bayyana siyan Carl Jenkinson dan shekaru 19 da haihuwa daga kungiyar Charlton.

Dan wasan wanda ya kware a bangaren baya ya takawa Charlton leda sau takwas ne kawai a kakar wasan bara, kuma ana iya amfani da shi a tsakiya.

"Ina fatan magoya bayan kungiyar Charlton za su fahimci dalilan daya sa na bar kungiyar. Wannan babbar dama ce ta zo gareni, amma har yanzu ina son Charlton a zuciyata," In ji Jenkinson.

"Ina matukar godiya da irin horon da Charlton ta bani tun ina dan yaro."

Jenkinson shine dan wasa na farko da Arsenal ta siya a hutun da ake yi, a yayinda kungiyar ta gaggara lashe kofi ko guda a kakar wasanni shida da suka wuce.