Fifa ta ce Ibrahim Chaibou zai iya ci gaba da aiki

Hakkin mallakar hoto Other

Hukumar kwallon kafa ta duniya, wato Fifa ta ce alkalin wasa dan kasar Nijar, Ibrahim Chaibou wanda ya hura wasan sada zumunci da Najeriya ta buga da Argentina zai iya ci gaba da aikinsa a yayinda take ci gaba da bincike.

Fifa dai tana zargin an yi coge a wasan, saboda ta lurra cewa anyi caca sosai akan za'a kara zura kwallo a wasan bayan Najeriya ta zura kwallaye hudu a ragar Argentina.

Alkalin wasan dai ya baiwa Argentina wani fenaritin da ake tababa akansa bayan wa'adin da aka debarwa wasan ya cika.

Fifa dai tace bazata iya dakatar da alkalin wasan ba, har sai ta kammala bincike.