Namibia ta kai karar Burkina Faso

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan da ake takkadama akansa dan asalin Kamaru ne.

Namibia ta kai karar Burkina Faso, Caf saboda amfani da wani dan wasa da bai cancanta ba a wasan share fage na taka leda a gasar cin kofin Afrika.

Hukumar Kwallon Kafan Namibia ta shaidawa Caf cewa dan wasan Burkina Faso Herven Zengue bai cancanci ya taka leda ba a wasan karkashin dokar Fifa.

Zengue dan asalin Kamaru ne, kuma ya bugawa Burkina Faso a wasan da ta doke Namibia da ci hudu da guda, wasan kuma daya fidda Namibia a cikin rukunin kasashen da za su taka leda a gasar cin kofin Afrika da za'a shirya a badi.

Dan wasan har wa yau ya buga wasan farko tsakanin kasashen biyu, inda Burkina Faso tayi galaba akan Namibia da ci hudu da nema.

Dokar Fifa dai ta haramtawa wata kasa amfani da 'yan wasan da ba nasu ba, sai sun nemi izinin sauya takardun shaidar kasarsu.