Kuruket: Anderson zai koma tawagar Ingila

James Anderson
Image caption James Anderson yana taka rawa sosai a gasar Kuriket

An sake kiran James Anderson zuwa tawagar kwallon Kuriket ta Ingila a wasan da za su fafata da Sri Lanka zagaye na uku wanda za a fara ranar Alhamis a Rose Bowl.

Dan wasan ya samu rauni ne a wasan farko da Ingila ta doke Sri Lanka, sai dai bai samu damar buga wasa na biyu ba.

Anderson na da damar nuna cewa ya warke sarai a wasan da Lancashire za su buga da Worcestershire a gasar Twenty20 ranar Lahadi.

Komawarsa tawagar Ingila na nuna cewa akwai yiwuwar ajiye daya daga cikin Stuart Broad da Steve Finn ko kuma Chris Tremlett.