Dan wasan Masar Elmohamady ya koma Sunderland

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ahmed Elmohamady ya taka rawar gani a Sunderland a kakar wasan bara, inda ya taka leda na wucin gadi

Sunderland ta kammala siyan dan wasan Masar Ahmed Elmohamady daga kungiyarsa ta ENPPI.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 23 ya takawa Sunderland din leda na wucin gadi a kakar wasan bara.

Dama dai kungiyoyin biyu sun kulla yarjejeniyar cewa idan dan wasan ya taka rawar gani, Sunderland za ta siye shi na din-din-din.

A yanzu haka dai dan wasan ya rataba hannu ne a kwantaragin da zai sa ya taka leda na tsawon shekaru uku a kungiyar.

Dan wasan shine na farko da Sunderland ta siya kafin kakar wasa mai zuwa, a yayinda dan wasanta Jordan Henderson ke shirin komawa Liverpool.