Man United ta sayi Phil Jones

Phil Jones Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Phil Jones yana cikin tawagar Ingila 'yan kasa da shekaru 21

Manchester United ta kammala sayen dan wasan Blackburn Rovers Phil Jones a farashin da rahotanni ke cewa ya kai fan miliyan 17.

Dan wasan na baya da ke taka leda a tawagar 'yan kasa da shekaru 21, ya kammala gwajin lafiya a United ranar 8 ga watan Yuni kafin a samu 'yar tangarda.

Duk da cewa kungiyoyi irinsu Arsenal da Liverpool sun neme shi, dan wasan mai shekaru 19 ya nace cewa ya fi son ya je Old Trafford.

Wata sanarwa da United ta fitar ta ce "ta yi murna" da kammala cinikin.

"Dan wasan ya kammala gwajin lafiya a makon da ya gabata sannan ya amince da kwantiragin shekaru biyar," a cewar sanarwar.

"Za a kammala cinikin da zarar dan wasan ya dawo daga tawagar Ingila."

Jones ya fara taka leda ne a gasar Premier a watan Maris din bara, amma ya taka rawar gani sosai, kuma ya buga wasan Ingila da Spain na 'yan kasa da shekaru 21 ranar Lahadi.