Alex McLeish ya yi murabus daga Birmingham City

Alex McLeish
Image caption Ana tunanin Alex McLeish zai iya komawa Aston Villa

BBC ta samu bayanan cewa kocin Birmingham City Alex McLeish, ya yi murabus daga kungiyar.

Birmingham wadanda suka lashe gasar cin kofin Carling a watan Fabreru amma kulob din ya fada gasar Championship a karshen kakar da ta gabata.

Mahukuntan kulob din dai sun bayyana cewa aikin Mcleish ba ya tangarda bayan da suka fadi.

Amma kocin dan kasar Scotland ya yanke shawarar barin kungiyar a kashin kansa.

Tuni dai aka fara alakantashi da komawa Aston Villa.