Murray ya kai wasan gab da kusa dana karshe

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Andy Murray

Andy Murray ya kai wasan dab da kusa dana karshe a gasar Tennis ta Aegon da ake yi a Queen's bayan ya doke Janko Tipsarevic.

Murray wanda shine na daya a Burtaniya a fagen Tennis ya doke Tipsarevic a wasanni uku da suka buga.

A yanzu haka dai Murray zai buga wasan kusa dana karshe ne da wanda ya yi nasara tsakanin Marin Clic ko kuma Thomaz Belucci.

Murray dai na buga gasar ne da raunin da ya samu a gasar French Open da aka kammala a makon daya gabata.