Andy Murray ya lashe gasar Queen's Club

Andy Murray Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Andy Murray shi ne na daya a Tennis a Burtaniya

Andy Murray ya lashe gasar Queen's Club inda ya doke Jo-Wilfried Tsonga domin shirya wa gasar Wimbledon Open.

Dan wasan na Burtaniya wanda ya taba lashe gasar a shekara ta 2009, ya yi nasara ne da ci 3-6 7-6 (7-2) 6-4, a gaban 'yan kallo 6,858.

Wannan ne karo na uku da aka yi wasan karshe a ranar Litinin a tarihin gasar, kuma tiketi 4,000 aka sayar cikin dare, inda jama'a suka rinka fitowa tun kusan karfe biyu na safe.

Wasu fiye da mutane dubu ne da basu samu damar sayen tiketin ba suka isa Queen's Club domin kallon wasan a majigi.