Panama ta kafa tarihi bayan ta doke Amurka

Adolfo Machado Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Adolfo Machado yana murnar kwallon da suka zirawa Amurka

Kasar Panama ta kafa tarihi bayanda ta doke Amurka da ci 2-1 a rukuni na uku na gasar cin kofin Gold Cup da ake yi a Amurkan.

Panama ta zira kwallaye biyun ne tun a zagayen farko na wasan ta hannun Luis Tejada da Gabriel Gomez wanda ya zira kwallo ta biyu daga bugun fanareti. Amurka ta mamaye zagaye na biyu na wasan, kuma a minti na 68 ne Clarence Goodson ya rama musu kwallo daya.

Haka nan 'yan wasan Amurka suka yi ta kokarin ganin sun rama kwallon da ta rage, amma abin ya ci tura saboda yadda 'yan bayan Panaman suka dage.

A yanzu Panama ce ke jagorantar rukunin da tazarar maki uku kan Amurka da Canada zuwa zagayen karshe na rukunin.