Ferguson ya so na ci gaba da wasa - Scholes

Paul Scholes
Image caption Paul Scholes ya taka rawa sosai a United

Paul Scholes ya bayyana cewa kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya nemi shi da ya ci gabada da takawa kulob din leda maimakon ritaya.

Dan wasan mai shekaru 36, wanda ya lashe gasar Premier sau 10 tare da United, ya bayyana ritayarsa ne a watan Mayun da ya gabata.

Scholes ya shaidawa BBC cewa: "Kocin ya yi tunanin cewa zan iya buga wasanni 15 zuwa 20 a kakar wasanni mai zuwa.

"Ba na jin karfi kamar yadda ya kamata a lokacin motsa jiki da kuma wasannin karshe na kakar da aka kammala.

"Na dauki wannan matakin ne wanda shi ne nake ganin ya fi dacewa da ni a yanzu."