Wasan Argentina ya kawo mana koma baya: Siasia

Image caption Kocin Najeria, Samson Siasia

Kocin Najeriya, Samson Siasia ya ce kasar ta buga kunnen doki ne da Ethopia saboda wasan sada zumuncin data buga da Argentina.

Najeriya ta buga biyu da biyu ne da Ethopia a Addis Ababa a wasan share fage na taka leda a gasar cin kofin Afrika da za'a buga a badi.

Bayan nasarar da Najeriya tayi akan Argentina da ci 4-1 a Abuja a ranar larabar data gabata, kasar ta isa Ethiopia ne wasu 'yan sa'o'i kafin a fara wasan..

"Yan wasan sunfi daukan wasan da suka buga da Argentina da mahimmacin a yayinda suka nuna halin ko'in kula a Ethopia." In ji Siasia.

"Wannan ya kowa mana koma baya matuka, sannan kuma 'yan wasan sun gaji abun da kuma yasa basu taka rawar gani ba".

Najeriya za ta sake karawa da Argentina a karo na biyu a wani wasan sada zumunci, wanda za'a shirya a Bangladesh a ranar 6 ga watan Satumba.

Samson Siasia dai ya ce yafi maida hankali ne a wasannin share fagen taka leda a gasar cin kofin Afrika da za'a shirya a bada.