Warner ya ki ganawa da kwamitin binciken Fifa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mataimakin Shugaban Hukumar Fifa da aka dakatar, Jack Warner.

Maitaimakin Shugaban Hukumar Fifa da aka dakatar Jack Warner ya ki ganawa da jami'an kwamitin Fifa dake bincike zargin cin hanci.

Ana dai zargin Warner da kuma abokin aikinsa Mohamed Bin Hammam wanda ya nemi kujerar shugaban Fifa, kafin ya janye da bada cin hanci dala miliyan guda ga membobin kungiyar hukumar kwallon kafa ta Caribbean.

Warner ya ce: "Ba'a a turo mun sammacin nema in gana da masu binciken ba, kuma bana niyyar yin hakan."

Warner da Bin Hammam dai sun musanta zargin aikata ba dai-dai ba.

Ana dai zargin membobin hukumar kwallon Caribbean su 25 da karbar cin hancin dala dubu arba'in kowannen su domin zaban Bin Hammam.