Sneidjder zai ci gaba da zama a Inter Milan

Image caption Wesley Sneijder na takawa Inter Milan leda

Wesley Sneijder ya kawo karshen cece kucen da ake yi akan makomarsa, yayinda ya yi nuni da cewa zai ci gaba da zama a kungiyarsa ta Inter Milan.

Rahotanni sun ambato cewa, kungiyar Chelsea da Manchester United na neman dan wasan mai shekarun haihuwa 27.

"Milan babbar kungiya ce, kuma ina matukar son ta." In ji Sneijder.

Dan wasan ya koma kungiyar Inter Milan ne daga Real Madrid a shekarar 2009, kuma ya taimakwa kungiyar a wannan shekarar matuka, inda ta lashe kofuna uku, wanda ya hada kofin gasar zakarun Turai.