Manchester City na gabda sayen Sanchez

alexis Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Alexis Sanchez

Mai kulob din Udinese a Italiya Gianpaolo Pozzo ya bayyana cewar Manchester City nada alamun sayen dan wasan Chile Alexis Sanchez daga wajensu.

Dan kwallon mai shekaru 22, rahotanni sun nuna cewar kudinsa ya kai fan miliyan 44.

Pozzo yace"Inter, Juve, Barca da Manchester City duk suna zawarcin dan kwallon".

Kwangilar Sanchez zata kare ne a Udinese a watan Yunin 2014,inda ya zira kwallaye 12 a kakar wasan data wuce kuma ya taimakawa kungiyar ta samu gurbin zuwa gasar zakarun Turai.

A farkon wannan watan, Inter Milan ta soma tattaunawa da Sanchez akan batun cefanarda dan kwallon.

City na kokarin siyo dan kwallo kafin a fara kakar wasa mai zuwa, amma dai abokiyar hammayarta Manchester United har ta riga ta sayo Phil Jones a Blackburn Rovers sannan tana gabda sayen Ashley Young daga Aston Villa.