Bazan koma Real Madrid ba-In ji Essien

essien
Image caption Essien na jin dadin kwallo a Chelsea

Dan kwallon Chelsea Michael Essien ba zai amince da duk wani tayi daga wajen Real Madrid ba, don ya bar Stamford Bridge.

Essien nada kwangila da zata dade a Chelsea kuma yace yana jin dadin taka leda a kulob din duk da irin rahotanni dake nuna cewar zai kara hadewa da tsohon kocinsa Jose Mourinho a Bernabeu.

Mourinho ya siyo dan Ghana din akan fan miliyon 24 daga Lyon a shekara ta 2005.

Wakilin Essien, Fabien Piveteau ya bayyana cewar"Micheal zai cigaba da kasancewa a Chelsea har zuwa shekaru hudu masu zuwa".

Ya kara da cewar "dan wasan na jin dadin taka leda a Chelsea".

A kakar wasan data wuce Essien yayi fama da rauni sannan kuma Chelsea ta kasance ta biyu a gasar Premier.