Zan zauna a Madrid na shekaru 10-Ronaldo

ronaldo Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ronaldo ya bar United a shekara ta 2009

Cristiano Ronaldo ya ce zai yi murna cigaba da kasancewa a Real Madrid har zuwa shekaru goma masu zuwa.

Ya koma Bernabeu ne daga Manchester United akan fan miliyan tamanin a shekara ta 2009 kuma ana alakantashi da Manchester City.

Sai dai dan kwallon mai shekaru 26 ya bayyana cewa "bana tunanin barin Madrid".

Ya kara da cewar "idan shugaban Madrid Florentino Perez yace mini in sanya hannu a kwangilar shekaru 10, zan rattaba hannu".

Dan wasan Portugal din ya zira kwallaye 53 a kakar wasan data wuce sannan ya lashe kofin Copa del Rey da sauran tawagar 'yan kwallon Jose Mourinho.

Rahotanni sun nuna cewar Manchester City na shirin bada fan miliyan 150 akan tsohon dan kwallon Sporting Lisbon kuma a shirye suke su bashi fan miliyan 21 kowacce shekara a matsayin albashi.