Ina jin dadin kwallo a Arsenal-Fabregas

fabregas
Image caption Cesc Fabregas

Kyaftin din Arsenal Cesc Fabregas ya bayyana cewar yana jin dadin kasancewa tare da Gunners kuma bai yanke shawarar barin kulob din ba.

Dan kwallon mai shekaru 24 an dade ana alakantashi da tsohuwar kungiyarsa wato Barcelona.

Fabregas yace"Ni dan wasan Arsenal ne, kuma na ji dadin zamana na shekaru takwas".

Ya kara da cewar"ban yanke shawarar barin kulob din ba amma dai abubuwa da yawa kan faru a rayuwa mutum ba zai iya fidda kauna ba".

Rahotanni daga Spain sun nuna cewar zakarun Turai wato Barca na bukatar akalla fan miliyan arba'in don siyo Fabregas.

Ya koma Arsenal ne daga Barca a shekara ta 2003 yana shekaru 16 da haihuwa kuma ana ganinshi a matsayin wanda zai iya maye gurbin Xavi wanda keda shekaru 31.

Amma a cewar Fabregas duk wata shawara akan makomarshi ta ta'allaka ne akan kocin Arsenal Arsene Wenger.