West Ham ta sayi Abdoulaye Faye

Abdoulaye Faye Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Abdoulaye Faye shi ne na farko da West Ham ta dauka

Sam Allardyce ya sayi dan wasa na farko bayan zuwansa West Ham, inda ya sayi dan wasan baya na Stoke City Abdoulaye Faye.

Dan wasan na kasar Senegal mai shekaru 33, Stoke sun shaida masa cewa ba za a sabunta kwantiraginsa ba a kakar bana.

Zai isa Upton Park a karshen wannan watan idan kwantiraginsa ta kare.

Allardyce ya dauki Faye a karo biyu a baya, bayan da ya dauke shi a Bolton da Newcastle.

"Na yi farin ciki matuka da zuwa na West Ham - domin ba karamin kulob ba ne, don haka ina fatan fara taka leda ba tare da bata lokaci ba," Faye ya shaida wa shafin intanet na kulob din.

"Ba ni da matsala a zuwa nan, wasu kungiyoyin sun neme ni, amma na fi son na zo nan".