Munason daukar bakuncin gasar Afrika a 2013

afrika ta kudu
Image caption Wasu 'yan kallo a gasar kofin duniya a Afrika ta Kudu

Shugaban hukumar kwallon Afrika ta Kudu-Safa Nematandani ya ce a shirye suke kasar ta maye gurbin Libya a matsayin wacce zata dauki bakuncin gasar cin kofin kasashen Afrika a shekara ta 2013.

Hukumar kwallon Afrika wato Caf ta bayyana cewar tashin hankalin dake faruwa a Libya ya janyo tana tunanin duba wata hanyar.

Nematandani ya ce Safa zata rubutawa Caf wasika don nuna sha'awarta a wannan makon.

A farkon wannan shekarar ne, Afrika ta Kudu ta dauki bakuncin da kwallon Afrika 'ya n kasada shekaru 21 sakamakon tashin hankali a Libya.

Wasu rahotanni dai sun nuna cewar an riga an baiwa Afrika ta Kudu damar daukar bakuncin gasar cin kofin Afrika na 2013, amma Nematandani ya ce ba haka labarin yake ba.

Yace"bamu samu wata takarda daga Caf ba akan haka, amma dai muna da sha'awar a bamu damar".

Sakamakon nasara daukar bakuncin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2010, yanzu haka dai an baiwa Afrika ta Kudu damar daukar bakuncin gasar kwallon Afrika a 2017.

Afrika ta Kudu dai ta nemi a bata damar daukar bakuncin gasar cin kofin Afrika a shekara ta 2015 amma sai Caf ta baiwa Morocco.