Jamus ta yiwa Ballack kora da hali

ballack
Image caption Micheal Ballack

Hukumar kwallon Jamus ta sanarda cewa kyaftin din tawagar 'yan kwallonta Micheal Ballack ba zai kara takawa kasar kwallo ba.

Ballack mai shekaru talatin da hudu da haihuwa ya bugawa Jamus kwallo a karawa 98 amma ya dade bai buga mata ba saboda rauni a idon sawunsa.

Ya kuma zira kwallaye 42 a wasannin daya bugawa Jamus tun daga shekarar 1999 amma bai taba lashe wata gasa ba tun da ya zama kyaftin.

Izuwa yanzu babu martanin da tsohon dan kwallon Chelsea ya bayyana game da sanarwar da hukumar kwallon Jamus ta fitar.

Kocin Jamus Joachim Loew ya cigaba da ajiye Ballack a matsayin kyaftin din tawagar duk da cewar ya kwana biyu bai buga mata kwallo.

Ballack a baya ya taka leda a Kaiserslautern da Bayer Leverkusen da Bayer Munich da kuma Chelsea.