Chelsea ta taya Modric na Spurs

Luka Modric Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Luka Modric ya haskaka sosai a Tottenham

Wakilin dan wasan Tottenham Luka Modric, ya ce tayin da Chelsea ta yi na sayen dan wasan kan fan miliyan 22 ya yi kadan.

Rahotanni sun nuna cewa Chelsea sun taya dan wasan mai shekaru 25 dan kasar Crotia sai dai Spurs sun yi watsi da tayin.

"Luka yana jin dadin zamansa a Spurs, amma idan wata dama ta zo wacce ta gamsar da kulob din da kuma dan wasan, to za mu tattauna," a cewar wakilinsa Nikky Vukan.

"A ra'ayi na, fan miliyan 22 ya yi kadan a taya wannan dan wasan."