Kamaru na zargin Eto'o da nuna rashin da'a

Samuel Eto'o Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Samuel Eto'o

Dan kwallon Inter Milan Samuel Eto'o da takwarorinsa biyu a Kamaru zasu fuskanci kwamitin da'ar hukumar kwallon kasar wato Fecafoot.

Sauran biyun sune dan Tottenham Benoit Assou-Ekotto dana Arsenal Alex Song.

Duka tuhumar da ake musu nada nasaba da wasan share fagen neman gurbin zuwa gasar cin kofin Afrika tsakaninsu da Senegal kafin a fara wasan.

Eto'o ya bayyana cewar "idan na aikata laifin daya shafi rashin da'a,to a hukunta ni".

An gayyaci Eto'o ne saboda bai shiga horo ba sakamakon rashin jituwa da Song sannan kuma ana zargin ya tsoma baki lokacin da aka canza wani dan kwallo a wasan da Senegal.

A wasan da suka tashi babu ci, Eto'o ya nuna a fili rashin jin dadinsa da aka cire Eric Maxim Choupo-Moting aka saka Henri Bedimo.

Shi kuma dan kwallon Arsenal Song ya gayyaceshi saboda tankiyarsa da Eto'o.

Shi kuwa Assou-Ekotto yayi laifi ne saboda kin amsa gayyatar bugawa kasar wasan duka da cewar an gayaceshi.

'Yan wasan uku an basu kwanaki takwas su maida martani akan batun.