Uefa:A Wembley ne za ayi wasan karshe na 2013

wembley
Image caption Filin wasan Wembley

Filin wasa na Wembley ne zai dauki bakuncin wasan karshe na gasar zakarun Turai a shekara ta 2013.

Hukumar kwallon kafa ta Turai Uefa wacce ta sanarda haka ta bayyana cewar an baiwa Wembley damar ce saboda a shekarar ce za ayi bukin cika shekaru 150 da kafa hukumar kwallon Ingila wato FA.

Shugaban Uefa Michel Platini yace"hakan na musamman ne don mutunta bukin zagayowar kafa FA".

An bayyana wasan da aka yi a filin Wembley a matsayin nasara.

Barcelona ce ta samu nasara a wasan inda ta doke Manchester United daci uku da daya a wasan da Lionel Messi ya haskaka.