Newcastle ta kammala sayen Demba Ba

Newcastle ta kammala sayen Demba Ba Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya taka rawar gani a West Ham bara

Newcastle United ta kammala sayen dan wasan Senegal Demba Ba daga kungiyar West Ham.

Dan wasan mai shekaru 26, wanda ya zira kwallaye 7 a wasanni 13 a West Ham a zagaye na biyu na kakar wasannin da ta gabata, ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru uku.

Kocin Newcastle Alan Pardew ya ce: "Demba ya taka rawar gani a West Ham bara, kuma zai taimaka mana sosai.

"Yana da karfi, ya kuma kware sosai musamman a sama."

Pardew ya bayyana aniyarsa ta sayen dan wasan a kokarin da yake yi na maye gurbin Andy Carroll wanda ya koma Liverpool a watan Janairu.