Fifa ta dakatar da Belize saboda tsoma bakin gwamnati

blatter Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sepp Blatter

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta dakatar da kasar Belize daga shiga harkar kwallon kafa a duniya saboda abinda ta kira "tsoma bakin gwamnati a harkar".

Wannan dakatarwar na nufin cewar watakila a haramtawa kasar shiga cikin wasanni share fagen neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da za ayi a Brazil a shekara ta 2014.

A wasan farkon neman zuwa gasar da za ayi a Brazil din, Belize ta samu galaba akan Montserrat daci biyar da biyu.

Fifa tace matakin ya wajaba saboda gwamnatin Belize ta ki amincewa ta bada kariyar tsaro ga 'yan kwallonta kasar da sauran jami'ai.

Kasashe 31 ne zasu tsallake zuwa gasar cin kofin duniya a shekara ta 2014 a yayinda za a buga wasanni 832 na share fage.