An sabunta: 19 ga Yuni, 2011 - An wallafa a 13:39 GMT

Obinna Nsofor ya koma Lokomotiv Moscow

nsofor

Nsofor yaci kwallaye takwas a West Ham

Dan kwallon Najeriya Victor Obinna Nsofor ya koma kungiyar Lokomotiv Moscow ta Rasha daga Inter Milan ta Italiya.

Dan wasan mai shekaru ashirin da hudu a ranar Asabar ya kulla yarjejeniyar shekaru hudu da kulob din.

Dan Super Eagles din ya tafi aro kungiyar West Ham ta Ingila a kakar wasan data wuce inda ya zira kwallaye takwas cikin wasanni 23.

Nsofor yace"kulob da dama sun nuna sha'awarsu amma Lokomotiv Moscow ce ta nuna da gaske take".

Ya kara da cewar"Na taka leda a Italiya da Spain da kuma Ingila amma zan samu kalubale na daban a Rasha".

Nsofor dai ya bugawa Najeriya wasanni 38 inda yaci kwallaye takwas, sannan ya buga gasar cin kofin duniya da Super Eagles a Afrika ta Kudu a bara.

A baya ya shafe shekaru uku tare da Chievo Verona kafin ya koma Inter Milan a shekara ta 2008.

A Najeriya kuwa ya bugawa kungiyoyin Plateau United da Kwara United da kuma Enyimba.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.