Watakila Tevez ya cigaba da taka leda a City

tevez Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Carlos Tevez

Akwai yiwuwar Carlos Tevez ya cigaba da kasancewa a Manchester City tunda ya bukaci iyalansa su zo daga Argentina, kamar yadda wakilinshi ya bayyana.

Tevez watan Disamban bara ne ya nema ya bar City saboda a cewarshi baya jin dadin zamansa a garin Manchester.

Amma bayan rahotanni sun nuna cewar an gayama Tevez cewar za a iya barinshi ya koma Argentina idan har ya kara wasu shekaru biyu a City, wakilinsa Kia Joorabchian ya ce a yanzu zai kwantar da hankalinshi a kulob din.

Joorabchian ya shaidawa jaridar Daily Star cewar"bana tunanin lamarin na kudi ne, batu ne iyali kuma yana kokarin warware matsalar".

Ya kara da cewar"ina tunanin a mako mai zuwa zai shawo lamarin kuma ya bada sanarwa".