Kocin Al Ahly Jose nason maye gurbin Shehata

shahata
Image caption Hassan Shehata

Manuel Jose kocin kungiyar Al Ahly ta birnin Alkahira na daga cikin masu neman mukamin zamowa mai horadda 'yan kwallon kasar Masar.

Masar ce ke rike da kofin gasar kwallon kasashen Afrika amma bisa dukkan alamu ba zata samu gurbin zuwa gasar Afrika da za ayi a badi ba.

Tsohon kocin kasar Hassan Shehata ya yi murabus ne bayan Masar ta tashi canjaras tsakaninta da Afrika ta Kudu a Alkahira abinda ya kara jefa kasar cikin rudu.

Ana saran mataimakin kocin Masar Shawki Gharib zai cigaba da jan ragamar kasar a sauran wasanni share fagen.

Ba a cimma yarjejeniya ba tsakanin hukumar kwallon Masar da Al Ahly, amma dai Jose na saran za a sasanta.