Sanchez ya tafi Spain don sasantawa da Barca

sanchez Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Alexis Sanchez

An baiwa Alexis Sanchez damar barin sansanin Chile na shiryawa gasar Copa America don zuwa Spain ya kulla yarjejeniya da Barcelona.

Rahotanni sun nuna cewar dan wasan Udinese din zai koma Barca akan Euro miliyan talatin.

Kocin Chile Claudio Borghi ya amince dan kwallon mai shekaru ashirin da biyu ya kamalla sasantawa da Barcelona kafin a fara gasar Copa America a ranar daya ga watan Yuli.

Kocin yace"idan bamu barshi ya tafi Spain ba, kuma aka kammala yarjejeniyar,zamu biya dala miliyon arba'in da biyar idan har wani abu ya faru dashi".

Sanchez ya haskaka a gasar Serie A a kakar wasan data wuce inda ya zira kwallaye 12 ya taimakawa Udinese ta samu gurbin zuwa gasar zakarun Turai.

Rahotanni sun nuna cewar Manchester United da Inter Milan da kuma Juventus duk suna zawarcin dan kwallon.