Gulf: McIlroy ya lashe gasar US Open

 Rory McIlroy
Image caption McIlroy ne dan wasa mafi karancin shekaru da ya lashe gasar tun bayan Bobby Jones a 1923

A karon farko dan kasar Ireland ta Arewa Rory McIlroy ya lashe babbar gasar Golf, bayan da ya yi nasara a gasar US Open.

McIlroy ya zamo dan wasa mafi karancin shekaru da ya lashe gasar tun bayan Bobby Jones wanda ya lashe gasar a 1923 kuma mafi karancin shekaru da ya lashe babbar gasa tun bayan Tiger Woods da ya lashe Masters a 1997.

Dan wasan mai shekaru 22 ya kafa tarihi a kan hanyar wannan nasarar da ya yi.

Dan kasar Australia Jason Day shi ne ya zo na biyu, yayin da Lee Westwood ya kare a mataki na uku.

Baya ga Westwood, Yang Yong-Eun na Koriya ta Kudu da kuma dan Amurka Kevin Chappell da Robert Garrigus su ne suka biyo baya.