Lyon ta kori Claude Puel a matsayin koci

Claude Puel Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Claude Puel

Kungiyar Lyon ta Faransa ta kori kocin 'yan kwallonta Claude Puel ba tare da bata lokaci ba.

Duk da cewar Lyon ta kamalla a matsayin ta uku a gasar Faransa a kakar wasan data wuce amma ta shafe shekaru uku ba tare da samun kofi ba.

Kulob kamar Lyon a Faransa wacce ta lashe kofin gasar kasar sau bakwai a jere wato daga shekara ta 2001 zuwa 2008 wannan sakamakon bai kai abinda ta saran samu ba.

Sanarwar da Lyon ta fitar ta ce "Lyon na sanarda da tafiyar Claude Puel wanda daga yanzu bai zai cigaba da kasancewa kocin 'yan kwallonta ba".

Korarsa ana saran zata janyowa Lyon hasarar akalla fan miliyan uku da rabi, kuma ana ganin cewar Remi Garde, wanda shine darekta kwallon matasan Lyon ne zai maye gurbinsa.