Algeria ta nada Halilhodzic a matsayin koci

Vahid Halilhodzic Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Vahid Halilhodzic

Hukumar kwallon kafa ta kasar Algeria ta sanarda Vahid Halilhodzic a matsayin sabon kocin 'yan kwallonta.

Tsohon dan kwallon Yugoslavia din ya kulla yarjejeniyar shekaru uku inda zai fara aiki a ranar daya ga watan Yuli.

Dan shekaru hamsin da biyar wanda ya maye gurbin Abdelhak Benchikha wanda aka kora bayan Morocco ta casa Algeria a wasan share fagen neman gurbin zuwa gasar cin kofin kasashen Afrika a shekara ta 2012.

Halilhodzic nada gogewa akan harkokin kwallon kafa a Afrika inda ya jagoranci Ivory Coast daga shekara ta 2008 da 2010.

A baya kuma ya kasance koci a kungiyoyin Lille da Rennes da kuma Paris Saint Germain.

Ya samu mukaminne a gaban tsohon kocin Jamus Jurgen Klinsmann da kuma na Brazil Carlos Dunga.